Mai Martaba Sarkin Lafiya kuma shugaban majalisar sarakunan jahar Nasarawa, Mai Shari’a, Sidi Bage Muhammad ya ce dawo da tsarin bai wa sarakuna hurumin kula da dazuka, zai taimaka wajen ganowa da hana batagari buya a daji suna aikata ta’asa kamar garkuwa da mutane da fashi da makami da dai sauransu.
Basaraken ya bayyana hakan ne yayin da hukumar tsaro da ba da kariya wa al’umma ta kasa a jahar Nasarawa ta kaddamar da wata hukuma da za ta kula da dazukan jahar.
Sarkin na lafiya ya ce hukumar za ta kuma taimaka wajen sasanta tsakanin manoma da makiyaya.
Mataimakin gwamnan jahar Nasarawa, Dakta Emmanuel Akabe ya ce gwamnati za ta ci gaba da mara wa hukumar baya don samar da tsaro a jahar.
Kwamandan hukumar Civil Dafence a jahar Nasarawa, Muhammad Gidado Fari ya ce jami’an sun sami horo na musamman ta yadda za su tinkari ‘yan ta’adda.
Ga wakiliyarmu Zainab Babaji da cikakken rahoton:
Facebook Forum