Gwamnatin jihar Flato ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar ta kafa dokar hana yawo na tsawon sa'o'i 24 sabo da barkewar wani sabon fitina a safiyar Alhamis wadda ya haddasa hsarar rayuka da dukiya masu yawa.
Kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar keftin Charles Okeocha wadda ya gaskanta aukuwar lamarin a hira da yayi da wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji, yace a safiyar Alhamis aka wayi gari da mutane daga sassan mazauna birnin suka fara cunnawa gidajensu wuta.
Keftin Charles, yace an sami hasarar rayuka da gidaje masu yawa da aka kona, amma ba zai iya bada adadi yanzu haka ba, sabo da suna ci gaba da bincke. Duk da haka ya ce sun shawo kan al'amarin.
Da yake amsa wata tambaya keftin Charles, yace an kama mutane masu yawa dangane da wan nan al'amari sai dai ba zai iya tantance yawansu ba ahalin yanzu.
Saurari: