Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Gidan Tunawa Da Tsohon Shugaban Kasar Ghana Kwame


Shugaban Kasar Ghana Ya Kaddamar Da Gidan Tarihi Domin Yawon Bude Ido
Shugaban Kasar Ghana Ya Kaddamar Da Gidan Tarihi Domin Yawon Bude Ido

Shugaban Kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo ya kaddamar da gidan tarihi domin karrama tsohon shugaban kasar Ghana marigayi Dr. Kwame Nkruma bisa irin mahimiyar rawar da ya taka wajen ci gaban kasar.

Gidan tarihin yana tsakiyar birnin Accra, inda Shugaban Kasar Ghana na Farko Dakta Kwame Nkrumah ya sanar wa Al’ummar kasar cewa kasar tayi nasarar samun 'yanci kanta a shekara ta 1957.

Tun daga lokacin ake kiran filin Kwame Nkrumah Memorial Park, wanda ya sa ya zama ɗaya daga cikin wurare 10 da aka fi ziyarta dan yawon bude ido a kowace shekara a Ghana.
A yayin da yake jawabi, shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo ya ce: " an kashe kudin Ghana sidi miliyan 13 wajen sake gyaran gidan tarihin, domin yana cikin tsare-tsaren gwamnati na mai da wurin ya zama mafi kyau wuraren yawon bude da abubuwan tarihi a yammacin Afirka baki daya.

Gidan tarihin na Kwame Nkrumah, wanda akalla kimanin mutane 90,000 ne suke kai ziyara a duk shekara kafin gyaran, yanzu ana sa ran cewa zai jawo masu yawon bude ido sama da miliyan 1 a duk shekara".

Taron bude gidan tarihin ya samu halartar Daraktan Bankin Duniya a Ghana Mr. Pierre Laporte da Ministan kudi Mr. Ken Ofori-Ata, kana da diyar marigayi Kwame Nkrumah Samia Nkrumah wace ta ce "Makomar 'yan Afirka tana bukatar haɗin kai. Don haka wannan wuri ne na haɗin kai, na zaman lafiya, da ƙarfi, da kuma abin alfahari da nuna ƙarfin baƙar fata. Na san muna tare da 'yan Afirka daga sassa daban-daban na duniya, kuma suna ciki aka aiwatar da wannan aikin kuma na yi farin ciki da cewa suna nan tare da mu a wannan taron".

Minintan kula da harkokin yawon bude ido da fasaha da Al’adu a Ghana Dakta Ibrahim Mohammed Awwal yace fatan su akan wannan matakin da suka dauka shine su janyo hankalin duk duniya . Ya kuma kara da cewa yana so kasar Ghana ta zama kan gaba a fannin yawon bude ido a duniya.

Mallam Hamza Attijani Masanin tattalin arzki kuma ya bayyana cewa bayan harkar noma da manya-manyan kamfanoni, abu na uku da ke kawo wa kasar kudaden shiga shine harkar bude Ido, kuma har idan gwamnati ta maida hankali taza samar wa kasar kudaden shiga masu dinbin yawa.

Saurari rahoton Hawa Abdul Karim

Kwame Nkrumah Memorial Park.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
XS
SM
MD
LG