A Litinin din nan, rikicin shugabancin Majalisar Dokokin jihar Legas ya dauki sabon salo bayan jibge dimbin jami’an tsaro a harabar yayin zamanta na yau.
An hange motoci da jami’an tsaron a ciki da wajen harabar ginin Majalisar Dokokin jihar legas din da ke yankin Alausa na birnin kasuwancin.
Gabanin zaman na yau, jami’an tsaro sun mamaye duk wata hanyar da ke kaiwa ga ginin majalisar.
An dan samu hatsaniya lokacin da wasu daga cikin jami’an tsaron suka yi kokarin kutsa kai cikin zauren majalisar.
Hakan ya janyo tsaikon sa’o’i a zaman majalisar na yau.
Dandalin Mu Tattauna