An dai kashe sojan saman mai mukamin Vice Marshall Hyon Yon Chol ne ta hanyar bindigewa. Daruruwan jami’an gwamnatin ne suka shaida hukuncin kisan, wanda aka aiwatar a ranar 30 ga watan Aprilu, kamar yadda mataimakin darektan hukumar tattara bayanan sirrin Han Ki-Beom ya bayyanawa kwamitin majalisar a birnin Seoul.
Kamfanin Dillancin labaran Korea ta Kudu na Yonhap, yace Mr. Kim, ya amince cewa baccin da Ministan tsaron ya yi, alama ce da ke nuna rashin biyayya da girmamawa. Ko da yake akwai rahotanni da suka nuna cewa Ministan ya sha kalubalantar Shugaba Kim kan wasu batutuwa da dama.
A Korea ta Arewa, Ministan Tsaro, shi ke da alhakin shirya huldar musanya tsakanin kasashe. Sannan kwamitin Tsaro da na dakarun Kasa su ke da alhakin yin tsare-tsaren al’amuran kasar.