Akalla sojojin tabbatar da zaman lafiya na MDD uku ne aka kashe a arewacin Mali mai fama da tashin hankali, a cewar tawagar MDD da ke aiki a kasar a jiya Lahadi.
Tawagar ta MINUSMA ta ce motarta ta hau kan wani bam din da aka dana a gefen hanya tsakanin birnin Gao da kauyen Anefis. Harin ya kuma raunata wasu sojojin na kiyaye zaman lafiya su biyar.
Babu wata kungiyar da ta dau alhakin kai wannan harin, to amma ya yi kama da irin hare-haren da kugiyar al-Kaida kan kai a yankin. Fada tsakanin kungiyoyi dabam-dabam masu dauke da makamai a arewacin Mali, wanda matattara ce kuma ta masu rajin jahadi, abu ne da ke yawan aukuwa.
An hallaka sojojin tabbatar da zaman lafiya sama da 100 a Mali, wanda hakan ya sa ya zama wuri mafi hadari cikin wurare 16 da sojojin MDD ke aiki a fadin duniyar nan.
Facebook Forum