Anji Mai Magana da yawun runudnar sojan Sudan ta kudu Philip Aguer ya cewa anyi gumurzun yaki yau litinin da hantsi, amma sojin Gwamnati ne ke samun galaba. Idan za’a tuna, wnanan yanki na Bentiu mai muhimmancin gaske ya fada hannun mayakan ‘yan tawaye a watan da ya gabata.
Majalisar Dinkin Duniya tana zargin mayakan ‘yan tawaye da laifin kisan daruruwan farar hula, ‘yan tawayen sun musanta zargin da ake masu na kisan farar hula.Ana wannan fafatawar ne kuwa kwanaki kadan bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya kai Juba a wani yunkurin ganin an kai ga samun zaman lafiya mai dorewa. Tattaunawar da ake yinta a kasar Ethiopia/Habasha.