Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gurfanad Da Barayin Itace Gaban Kotu


An gurfanad da bayayin itace a jihar Taraba A Najeriya
An gurfanad da bayayin itace a jihar Taraba A Najeriya

Yan ci ranin kasar China da dama ne ke kwarara yankunan Gasol,Bali, Ardokula,Kurbi, Donga, da Wusa dake jihar Taraba don aikin fasa kwbrin madubiya wadda aka danganta darajar ta nan a biyu baya ga manfetur a kasuwannin kasar China.

Yan ci ran na anfani da kauyawa mazauna yankunan wadan da basu san darajar itaciyar madubiyar ba, tare da taimakon yan kudancin Najeriya wajen safarar itatuwar cikin manya-manyan motoci da daddare zuwa bakin tekunan kasar Najeriya.Inji Alhaji Abubakar Mamud wani mazaunin Bali na jihar Taraba.

‘’Da mu dai bamu dauki itayuwan suna da muhimmaci sosai ba, a’a, itaciyar mmuna kiran shi madubiya idan mace ta haihu idan ta samu matsalar jini sai a sassaka bawon itaciyar a jika sai a bata tasha, daga baya sai muka ga wasu sunzo suna neman irin wannan itace, da zuwan su bamu dauki neman itacen wani abu ba, wani zaizo yace yana so sai suba mai unguwa kamar dubu 20 ashe mu ba musan cewa suna kwasan garabasa bane itacen nada muhimmamci kwarai da gaske.’’

Honarabul Yusuf Ibrahim dan majilisar dokokin jihar mai wakiltan mazabar Gasol na 2 ya tabbatar da wannan batu na fasa kwabrin wannan itace a yankunan da yake wakilta.

‘’Sunana Yusuf Ibrahim ina wakiltan Gasol ta 2 tabbas haka ne akwai baki daga kasashen waje musammam daga China an kawo korafi a majilisa kuma munyi zama akai, a matsayin mu na yan majilisa mu mun hana mun bada umurni cewa bangaren zartaswa ya tabbatar cewa an hana daukar wannan itace, dokar da kuma muke son muyi shine idan ka sare kwaya daya to ka dasa kwaya hudu, ba shakka a doka kan an hana kuma an daina sai dai wasu sukan bi cikin dare kuma su sari wannan itaciyar kuma su fita dasu da daddare.’’

Gwamnanjihar Taraba Akitek Darious Dickson Isiyaku ya tabbatar da cewa yanzu haka akwai mutane bakwai dake huskantar sharaa sakamakon tuhumar su da aikin fasa kwabrin itaciyar na madubiya da yayi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

‘’Shi itacen nan har yanzu ba a daina yankar sa a daji ba, muna nan dai mutanen mu suna bin su a daji har yanzu amma idan ALLAH ya yarda matsalolin sare wadannan itatuwan ya ragu kwarai da gaske mutane kamar su 7 yanzu haka nun gurfanad dasu a kotu kan wannan batu, idan mutum yana son ka yanki itacen kazoo mu baka lasisi kuma zamu nuna maka inda zaka yanka itacen bayan ka sare itacen sai ka dasa wani, mu zamu baka irn da zaka dasa sabo da shekara biyar zuwa bakwai nan gab aka sake zuwa ka sara, sabo da muna tsoron idan zaizayar kasa ya zo ba tare da an dasa wasu itatuwan ba to ba zamu iya yin noma ba, to kaga za a samu babban matsala Kenan.’’

Daya daga cikin masu sanaar sayar da katako Mallam Babangida mai Katako ya bayyana yadda yan fasa kwabrin itaciyar na madubiya ke fasa kwabrin itaciyar zuwa kasar china.

‘’Akwai bakin da ke shigo muna sunas fasa wadannan itatuwan suna saran su a boye ba tare da sanin hukuma ba idan sun shigo suna hada baki ne da yan gari sai suyi shigar burtu su bace sai nu nemi yaran gari inda ake biyan naira biyar sai su bada 20 inda ake biyan 20 kuma su bada 100.’’

Yayin da al’ummar jihar Taraba ke jiran suga tanade-tanade da dokar sare itacen madubiya zata tanada.

Ga Sanusi Adamu da Karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG