Akwai bukatar shirya manufofi da za su sanya wannan sashi na bunkasa hada-hadar kasuwanci zuwa tasashoshin teku, kuma ina ganin hadakar hukumar kasuwancin ta yankin Afurka na da gagarumar rawa da za ta taka wajen samun wannan nasara.
Inji jami’a daga kungiyar bunkasa lamuran kasuwanci ta majalisar dinkin duniya Lousiania Rodrizue, a taron bunkasa tashoshin teku don kasuwanci a Afurka ta yamma da Afurka ta tsakiya da aka gudanar a Abuja.
Rodrizue ta ce gudanar da wannan jagoranci shi zai kawo tururuwar ‘yan kasuwa ga tashoshin tekun na Afurka da zai sanya sashen ya rika samar da makudan kudin shiga.
Hakanan taron ya zanta kan inganta tasoshin bakin tekun ta hanyar saukin gudanar da kasuwanci da hana tsoma bakin wadanda doka ba ta ba wa izini ba da kan wahalar da hada-hadar.
Taron ya samu halartar wakilai daga kasashen Afurka da kwararru daga sauran sassan duniya kan lamuran kasuwancin teku.
Domin karin bayani, saurari Rahoton Nasiru El Hikaya...
Facebook Forum