Matsalar barace-barace da sunan Almajiranci na ci gaba da jan hankalin manazarta da masu ruwa da tsaki, game da yadda za a kawo karshen al'amarin a Najeriya.
Cibiyar adana kayan tarihi da al'adu da kuma bincike da ke karkashin jami'ar Amadu Bello ta Zaria, ta shirya taro na musamman don shawo kan kalubalen da ke rataye da maganar Almajiranci.
Farfesa Ahmed Modibbo Mohammed na jami'ar Amadu Bello ya gabatar da mukala mai taken "Kafin hana tsarin ilimin Almajiranci a Najeriya" kuma ya ce, wajibi gwamnati ta tashi tsaye wajen shigar da tsarin karatun boko da na allo.
Dr. Salisu Bala, malamin tarihi a jami'ar Amadu Bello ya nuna da bukatar kula da ilimi, muhalli da lafiyar Almajirai don magance barace-barace a Najeriya.
Wakiliyar Gwamnan jahar Kaduna Hajiya Amina Adamu Ikara, wadda ita ce babbar sakatariya a hukumar bada ilimi na bai daya a jahar Kaduna, ta ce, gwamnatin jahar Kaduna ta yi nisa wajen gudanar da makarantun allo ta hanyar zamani.
Sai dai kuma tsohon gwamnan jahar Kaduna Alh. Muktar Ramalan Yaro, ya ce, rashin halarta gwamnoni da sarakuna da malaman addini ya tauye wannan taro.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka a Kaduna, Isah Lawal Ikara.
Facebook Forum