Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Gangamin Sauyin Yanayi A Amurka


Ana nuna adawa da rashin kulawa da batun sauyin yanayi na shugaba Donald Trump a Amurka

Dubbun dubbatan masu hankoron kare yanayi sun yi gangami a Washington DC, babban birnin Amurkayau asabar, a wani yunkurin samun goyon baya ko kuma jawo hankalin duniya ga matsalolin da suka danganci yanayi.

Wadanda suka shirya wannan taro sun ce taron da aka lakawa suna jerin gwanon mutane akan yanayi an shirya shi ne yazo ranar daya da cika kwanki dari da hawan shugaba Donald Trump kan garagar mulki.

Wadanda suka shirya gangamin sunyi Allah wadai da abinda suka dauka ko kuma suke gani tamkar rashin kulawa da matsalolin yanayi da gwamnatin Trump ke yi.

Suk ace manufofin gwamnatin Trump masifa ce ga yanayi da kuma al’umma musamman talakawa, tsiraru wadanda ba turawa bane.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG