Mutane sun dauki wannan matakin ne bayan da babban mai shari’ar kasar ya ce an baiwa Alkalai biyar da ke sauraron karar cin hanci.
A ranar Litinin ne aka kai karar gaban hukuma mai yaki da cin hanci a kasar, abin da ya yi sanadin soma wannan zanga-zangar a manyan biranen kasar uku.
Kimanin mutane 50,000 suka taru a babban birnin kasar Lilongwe, inda wasu tsiraru kuma suka taru a birnin Blantyre da Mzuzu.
Shugabannin adawa sun ce, anyi zamba a zaben da aka gudanar a ranar 21 ga watan Mayun bara, inda Mutharika ya yi nasarar doke abokin karawarsa Lazarus Chakwera da dan tazarar da bai taka kara ya karya ba.
A watan Agusta, shugabanin adawar suka kalubalanci babbar kotun Malawi a bisa sakamakon zaben, wannan shine karon farko a Malawi da za a kalubalanci zaben shugaban kasa a kotu tun da kasar ta samu ‘yancin kai daga Birtaniya a shekara ta dubu daya da dari tara da sittin da hudu.
Facebook Forum