Gwamnatin dai tace ta dauki wannan matakin ne bisa la’akarin yawan jama’ar dake kara kwararowa zuwa jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar Alhaji Danladi Ndayebo ya fadi cewa yawan tashe-tashen hankulan dake faruwa a wasu jihohin dake kusa da su, ya kawo cinkoso. Shiya sa suka yanke shawarar yin sabon asibiti musamman na mata masu ciki kuma kwanan nan za a kaddamar da shi.
Kwamishiniyar kiwon lafiyar jihar Hajiya Hadiza Abdullahi tace sabon asibitin da suka so kamalawa tun a watan Disambar bara, zai maida karfine akan mata masu juna biyu.
Duk da yake samar da wannan asibiti ya zo ne a daidai lokacin hada-hadar siyasa, masana sun yi imanin cewa zai taimaka wa mata dake samun matsaloli wajen haihuwar wanda har ma akan rasa rai.