Wasu kungiyoyin addinai na Musulmai da Kiristoci a yankin Arewa maso yamma a Najeriya sunyi babban kira ga al’uman Najeriya, da suyi la’akari da abun da ke faruwa kada su sa kansu wajen abun da zai maida kasar baya. Kasan cewar kasar ta kowa da kowace kuma babu wani adini ko kabila da ke da kasar.
Wadannan matasan su gudanar da wani taro don wayar da kan al’umah, Pasto. Gebral Osabemijoso, yayi kira da cewar yakamata ‘yan Najeriya, su hada kansu su bar banbance banbance addinai su sani fa cewar wannan kasar tasuce, kuma suyi zabe ba dan suna addinni daya da ga cikin 'yan takara ba, suyi zabe bisa abinda suka amince dashi badan babancin addini ba.
Ya kara da cewar duk wanda yayi ma al'uma aiki sun sanshi kuma wanda baiyi ba sun sani, don haka mutane su lura su zabi wanda ya dace. Ta bakin Komared Idris Salisu Rogo, sakatare janaral na gamayyar kungiyoyin matasan Najeriya masu tarzoma a lokacin zabe, yace dolene su fahimci cewar su ‘yan Najeriya ne da musulmi da kirista don haka yakamata su zo su hada kansu guri daya.
Suma dai suyi Allahwadar da dage wannan zabe da akayi , kuma sunce duk wani dan siyasa dazai zo kamfe to yakamata yanzu yazo yayi kamfe da irin aikin da yayi ba da addininsa ba. Shima Mal. Aminu Bello Usman, yace babban abun da ke haifar da rashin zaman lafia a lokaci da bayan zabe a Najeriya shine rashin gaskia a wurin hukumar zabe rashin gaskia a wajen jami’an tsaro da su kansu masu yin zaben, da shuwagabanni. Don haka suna kira da al’uman Nageriya yakamata su lura da duk wani abu da zai kawo tashin hankali a kasar don magance ta.