Zaben zai fi maida hankali ne a jihar Michigan mai muhimmanci dake tsakiyar yammacin kasar, inda kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a ke nuna tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden na kan gaba, yayinda dan majalisar dattawan Vermont, Bernie Sanders ke biye da shi.
Michigan ita ce babbar mai bada kuri'a a zaben na yau Talata inda wakilai 125 zasu kada kuri’ar.
Sanders shine ya lashe zaben fidda gwani a shekara 2016 a Michigan amma zaben na ‘yan kwanakin nan ya nuna Biden na samun rata mai yawa.
Ana kuma zabe a jihohin Washington da Missouri da Mississippi da Idaho da kuma North Dakota
Wannan ita ce fafatawar farko tun bayan zaben "Super Tuesday" a makon jiya da aka yi a jihohi a lokacin da tsarin zaben ya sauya daga zaben kananan jihohi zuwa gudanar zabe a jihohi da dama a lokaci guda a fadin kasar.
Facebook Forum