Gidauniyar Harkokin Musulincin ta Najeriya, wato IDN a takaice, da hadin gwiwar kungiyar ci gaban matasa ta jihar Kano sun shirya wani taron lacca a Kano domin wayar da kan jama’a musamman matasa kan muhimmancin zaman lafiya da kuma kaucewa tashe-tashen hankula.
Babban makasudin taron laccan shine fadakar da jama’a masamman, matasa, game da illar da ke tattare da aikata miyagun aiyuka da tada hankulan jama’a, masamman ta la’akarin da yadda Najeriya, ke tun karan manyan zabubbukan siyasa.
Abubakar Mukhtar Salisu, daya daga cikin wadanda suka shirya laccan yace Kungiyar bunkasa addini Musulunci ta IDN, tayi nazari bisa abubuwa marasa dadi dake faruwa a cikin aluma ta hanyoyin daban-daban, karmar kai hari ga masallaci da kuma Coci, wanda yace ko kusa baida alfanu.