WASHINGTON, DC —
Jami’an ‘yan Sandan rundunar jihar Ogun, sun damke wasu matasa biyu da ake zargin su da yiwa wata matashiya mai tallar Gwanda, mai shekaru ashirin da ukku, fyade.
Matasan Eziekel Yusuf, mai shekaru ashirin da tara da Musa Abubakar, mai shekaru ashirin da biyar, sun yaudari matashiyar ne zuwa wani gida da niyyar cewa zasu saye Gwanda.
Kakakin ‘yan Sandan jihar ta Ogun, Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da labarin yace ihun da matashiyar tayi shi ya ja ra’ayin mutane har suka kaimata dauki daga bisani batun ya kai ga ‘yan Sanda.
Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Ahmed Iliyasu, ya bada umarin a tura maganar ga sashen binciken yaki da fataucin mutane na rundunar domin a gudanar da cikakken bincikeakan lamarin.