Rundunar tsaro da bada kariya wa al’umma ta kasa Civil Defence a jihar Nasarawa ta ce ta chapke Ahmadu Yaro da ta ke zargi da yi wa wata jinjira ‘yar watanni uku fyade a garin Adogi dake jihar Nasarawa.
Kwamandan rundunar Civil Defence a jihar Nasarawa, Muhammad Gidado Fari ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Uban jinjirar, Ali Hashimu ya ce yarinyar na samun kulawa a asibiti.
Shugaban kungiyar ‘yan jarida mata a jihar Nasarawa, Hadiza Umar Aliyu ta ce tun lokacin da suka sami labarin fyaden suke fafutukar ganin hukumomi sun dauki mataki.
Shugaban kungiyar mata lauyoyi reshen jahar Nasarawa, Alu Justina Alkali ta ce za su bi diddigi har sai yarinyar ta sami adalci.
Kwamishinan harkokin mata da samar da walwalar al’umma a jahar Nasarawa, Halima Jabiru ta ce gwamnati na kokarin kau da dabi’ar fyade a jihar.
Saurari karin bayani a sauti:
Facebook Forum