Barayin mashin tsakanin Nigeria da Jumhuriyar Niger sun bullo da dabaran anfani da wani sinadari domin karbe mashin daga mutane.
Wadannan barayin dai suna shaka wa masu hayan babur wadanda aka fi sani da suna kabu-kabu wannan sinadarin, wanda zaisa su fita hayyacin su.
An fara wannan danyen aikin ne a birnin kwanni, zuwa garin Illela dake cikin jihar Sokoto, inda akan hanya sukan shaka wa wadannan ‘yan kabu-kabu wannan sinadarin.
Ga Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Facebook Forum