Kakakin hukumar dake yaki da fataucin ko safarar mutane ta Najeriya Mr Josiah Emerem ya bayyana makasudin samun dokar kwarmata labarin safarar mutane.
Yana mai cewa mutane da dama ba sa iya kai rahoton fataucin mutane kamar yadda a keyi da sauran laifuka. Rashin dokar na takaita ma hukumar samun rahotanni aika aikar da ake tafkawa a kasar.
Dokar kwarmata a bangaren cin hanci da rashawa da zarmiya da yiwa tattalin arziki zagon kasa na samun nasara sosai. Inji kakakin dalili ke nan da hukumarsu ta zabura ta nemi gwamnatin tarayya ta aiwatar da dokar domin a dinga kwarmata bayanai kan masu safarar mutane. Yin hakan zai karfafa 'yan Najeriya su ji karfin kwarmata wa hukumar bayanai.
Dr Abubakar Umar Kari na Jami'ar Abuja yace matakin zai taimaka gaya wajen dakile fataucin mutane a Najeriya musamman a wasu jihohin kudancin kasar inda ake fita da yara mata waje a tilasta masu shiga karuwanci.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum