Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bankado Sama da Fadi na Fiye Naira Miliyan Dubu 200


Kwamitin da Gwamnatin jihar Filato, ta kafa domin bincken aiyukan Gwamnatin da ta shude ta Jonah Jang, ta bankado fiye da Naira miliyan dubu 200, da aka yi sama da fadi dasu.

Da yake mika rahoton shugaban kwamitin kuma mataimakin Gwamnan jihar Filato, Farfesa, Sony Tyoden, ya bayyana cewa sun gano cin hanci da almubazaranci da kudaden jama’ar jihar Filato, da rashin bin doka wajen fitar da kudaden.

Shugaban kwamitin yace karo na biyu na Gwamnatin da ta shige ya cika ne da rashin gaskiya da nuna bangaranci da sanya mutane kalilan wajen gudanar da harkokin mulkin jihar.

Yace misali akwai wani mutun guda, dan na iya wanda ya nada kansa matsayi ukku, shine mai tattara dukkan bayanai, shine mai gudanar da harkokin biyan albashi kuma shine janar manaja, duk a lokaci guda.

Shugaban kwamitin yace sun gano cewa Gwamnatin da ta shude ta bar bashin Naira miliyan dubu 222.3, sabanin miliyan 103, da Gwamnatin Jonah Jang, ta mika a rubuce a takardar mika mulki.

Ya kara da cewa Gwamnatin da ta shude tayi ikirarin kashe Naira miliyan dubu 8.6, wajen gina sabon gidan Gwanati, amma kwamitin ta gano cewa an kashe Naira miliyan 16.4, ne kuma har yanzu ba’a gama aikin ba.

Yace babban Bankin Najeriya, ta baiwa asusun jihar Filato, Naira miliyan dubu biyu, dan ingata kananan masana’antu a jihar, amma kashi tasa’in na kudin da aka bayar ranar 17, ga wata Maris, na wannan shekarar, an kwashe su ne a cikin kwanaki biyu, kuma babu wata masana’anta da ta amfana da kudin.

Da yake karbar rahoton kwamitin Gwamnan jihar Filato Simon Lalong, yace Gwamnati ta baiwa duk wanda yasan ya nada hannu a wannan badakalar mako biyu, ya kawo kansa.

Yana mai cewa “bana son wani yazo yana roko na in yakama hanyar gidan kurkuku, yace shima abunda yake bukata ayi masa kennen in ya bar karagar mulki.”

XS
SM
MD
LG