Yayin da hukumomi da kungiyoyi da kuma daidaikun jama’a ke cigaba da taimaka ma ‘yan gudun hijirar Boko Haram kamar yadda ake ta kiraye-kirayen a yi, wasu bata-gari na rabewa da tausayawar da ake yi sun a damfarar. Wadannan mayaudarar kan yi karyar cewa su ‘yan gudun hijira ne ko kuma ‘yan kungiyar tallafa ma ‘yan gudun hijirar.
Dubun irin wadannan matan ya cika a Taraba yayin da aka nemi kai su inda su k ace suna son zuwa inda ‘yan gudun hijira su ke amma kuma daga baya su ka noke. Matan, wadanda su k ace su ‘yan garin Mubi ne su ka zo fadar hedikwatar jahar Taraba neman taimako, sun sami taimakon, to amma daga baya kuma asirinsu ya tonu.
Wakilinu na shiyyar Adamawa Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito wata daga cikin matan da ake zargi na ikirarin cewa ta kai ziyara a wuraren da marayu ke zama a sassan arewa maso gabashin Najeriya da ma kasar Kamaru.
Ga wakilinmu Ibrahim Abdul'aziz da cigaban labarin: