Bayan wata ganawar sirri ta sa'a daya da su ka yi sakamakon wani sabani da aka fara samu a zauren Majalisar Dattawan Najeriya, an ba Shugaba Mohammadu Buhari damar karbo bashin da ya nema na dalar Amurka biliyan 23, kwatankwacin Naira triliyan 8 da digo 5.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan, shi ne ya karanta jerin basussukan daya-bayan-daya har aka kai lokacin da majalisar ta amince da su amma sai da aka yi wata 'yar mujadala da Shugaban Marasa Rinjaye Sanata Einyinanya Abaribe, har sai da majalisar ta shiga wani zaman sirri na sa'a daya.
Bayan sun koma zaman na Shugaban Kwamiitin Kula da ayyuka na Musamman, Sanata Yusuf Abubakar Yusuf ya ce basussukan ba na aljihun gwamnati ba ne, an bada su ne domin yin manyan ayyuka kamar hanyoyin jirgin kasa, da batun samar da wutar lantarki na Mambila da manyan tituna wadanda za a sa wa shingen tollgate domin samun kudaden shiga.
Da ta ke amsa tambayar yawan basussuka da kungiyoyi masu zaman kansu da ma babban bankin Najeriya suke korafi akai, Ministar Kudi da tsare-tsare Zainab Shamsunah Ahmed ta ce basussukan ba su yi yawa ba, rashin fahimtar mutane ke janyo korafe-korafen.
A wani kiyasi na baya-baya, an ce Najeriya ta na da bashi da ya kai Naira triliyan 26.2 a kanta a kwatar karshe ta shekarar 2019.
Ga karin bayani cikin sauti.