Alhamis 28 ga watan Nuwamba, Amerkawa ke gudanar da bikin yiwa Allah godiya da samun sabuwar kasar Amurka. Bikin da a turance ake kira Thanksgiving da Turanci.
Wannan ranar ta hutu ce a fadin Amurka inda Amurkawa na shakatawa tare da cin abinci da gudanar da tarukan tuntubar juna da zuwa kantuna tare da iyali domin sayen kayan marmari.
Wannan buki na cika-ciki na zuwa da al’adu iri-iri; wanda daga cikinsu shi ne tafiya a hadu da ‘yan’uwa na jini da abokai.
Kamar yadda suka saba ana haduwa da ‘yan’uwa da abokai a ci abinci, da kallon fareti da kwallon kafa da sauransu.
Hakazalika iyalai da abokai kan hadu waje guda a gasa talo-talo.
Ga wasu kuwa lokaci ne na hutu da fara yin sayayya musamman na Kirsimeti.
Ana kuma gudanar da shaharren paratin Macy Day's a fadin kasar da ka iya jan miliyoyin 'yan kallo.
Ana kiyasin mutane miliyan 49 ne za su yi tafiye-tafiye gabanin wannan hutun, wanda hakan ya dara na bara da miliyan guda; don haka ya zama bukin cika ciki mafi armashi cikin kusan shekara 10.
Dandalin Mu Tattauna