Shugaban Amurka Donald Trump ya ce lokaci ya yi da ya kamata su hada kai da Mexico, su “kaddamar da yaki” akan gungu-gungun masu safara muggan kwayoyi da ke gudanar da ayyukansu a kudancin iyakokin kasashen biyu.
Kiran na Trump na zuwa, bayan wani harin kwantan-bauna da ya rutsa da wasu Amurkawa ‘yan gida daya, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla kananan yara shida tare da wasu mata uku.
Shugaban na Amurka ya ce, mutanen sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da fadan bindiga ya kaure tsakanin wasu gungu-gungun masu safarar muggan kwayoyi, yana mai cewa, idan Mexico na bukatar taimako wajen kawar da su, Amurka a shirye take ta taimaka.
Sabon shugaban Mexico, Andres Manuel Lopez Obrador, ya shiga shafin Twitter, ya godewa Trump bisa wannan tayi, yana mai jaddada cewa, za su tabbatar an bi diddigin wannan lamari tare da bi wa wadanda aka kashe kadinsu.
Facebook Forum