Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Son A ladabtar Da Koriya Ta Arewa Sabo Da Harba Roka


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice take magana da manema labarai kan Koriya Ta Arewa, ranar Laraba.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice take magana da manema labarai kan Koriya Ta Arewa, ranar Laraba.
Amurka tace tana son ganin an dauki “matakan ladabtarwa” kan Koriya ta Arewa sabo da harba roka data yi, domin haka Washinton ta ci gaba da cewa, zata bukaci kasa da kasa ta dauki mataki cikin kwanaki masu zuwa.

Jiya laraba, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harba rokar, ya kira matakin,a fili yake cewa hakan ya kaucewa kudurin majalissr dinkin duniya, wanda ya haramtawa Pyongynag aiwatar da duk wani irin gwaji na makamai masu linzami dana Nukiliya.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice, tace sanarwar da ta fito daga kwamitin itace wacce kwamitin ya bayar ba tare da bata wani lokaci kuma mai karfin gaske da kwamitin mai wakilai 15 ya bayar.Madam Rice tace Amurka zata yi aiki da hukumomin kasa da kasa domin cimma matsaya kan mataki da ya kamata a dauka kan Koriya ta Arewa. Tace zata duba gurori masu ma’ana a zahiri da zasu hada da ladabtarwa.

Haka kuma Rice tace, matakin da Koriya Ta Arewa ta dauka, a fili ya jawo shakku kan dukufar kasar na komawa kan teburin shawarwari, da suka kunshi kasashe shida dangane da shirin nukiliyar kasar.

Ranar laraba, Koriya Ta Arewa ta bada sanarwar ta chulla roka mai cin dogon zango, wacce kasar tace ta kunshi tauraruwar dan Adam da zai rika kewaya duniya.
XS
SM
MD
LG