Da yake magana jiya jumma’a a nan birnin Washington, Hagel ya bayyana cewa, shirin ya kunshi kafa wata tashar na’urar hangen makamai ta rada a Japan , ya kuma ce za a yi haka ne ganin ci gaban da Koriya ta Arewa ke samu a fasahar makaman nukiliya.
Bisa ga cewarsa, Amurka ta riga ta girke shingayen kare makamai masu linzami guda talatin a jihohin California da Alaska kuma sababbin tashoshin zasu fara aiki a shekara ta dubu biyu da goma sha bakawai.
Koriya ta arewa ta yi barazanar shiga yakin Koriyawa na biyu tare da amfani da makaman nukiliya a matsayin maida martani kan takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Pyongyang sakamakon gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango da tayi a watan Disamba, da kuma gwajin makamin nukiliya karo na uku da tayi watan da ya gabata.