Ana zargin wasu ‘yan kasar China biyu da yin kutse a ayyukan daruruwan kamfanoni a fadin duniya, ciki har da kamfanin nazarin halitta da suke kokarin fitowa da maganin rigakafin COVID-19 da kuma jinya, yayin da suke aiki da ma’aikatun tsaron China.
Ana zargin Li Xiaoyu mai shekaru 34 da Dong Jiazahi mai shekaru 33 da aikata laifuka 11 a gundumar gabashin jihar Washington a ranar Talata, karon farko da masu shigar da kara a Amurka suka zargi masu kutsen China da aikata laifi da suka bayyana da babbar barazana na yin aiki da kasar China, yayin da kuma ake auna kamfanonin domin biya bukatun kai.
John Demers, shine shugaban sashen tsaron kasa a ma’aikatar shari’a ta Amurka, ya zargi China da taimakawa masu aikata laifin kutse.
Yanzu China ta dauki gurbinta tare da Rasha da Iran da kuma Korea ta Arewa, a cikin kungiyar kasashe masu abin kunya da ke bada kariya ga masu kutse don su kuma miyagun su bada bayani masu amfani ga kasar China domin ita ma ta baiwa jami’iyar kwaminisanci mai mulkin China, wacce take neman fasahar kamfanonin Amurka da kamfanonin da ba na ‘yan China ba ruwa a jallo, ciki har da masu nazari a kan COVID-19, inji Demers a wani taron manema labarai.
Facebook Forum