Jiya Asabar wani babban wakilin Amurka a wurin tattauna kan yanayi Peru, ya yi gargadi ga masu tattaunwar da ta cije, cewa muddun aka kasa cimma maslaha nan ba da jimawa, kan adadin carbon da ke gurbata yanayi, hakan zai rage damar da ake da ita ta cimma yarjajjeniyar kasa da kasa a shekara mai zuwa a birnin Paris.
Wakilin Amurka kan batutuwan yanayi Todd Stern, ya yi gargadin nasa ne bayan da masu tattaunawa daga kasashe sama da 190 su ka kasa cimma daidaito na sharar fage, a tsawon kusan makonni biyun da su ka yi su na tattaunawa, wadda za a kawo karshenta ranar Jumma'a. Zuwa jiya Asabar an shiga rana ta 13 da fara tattaunawar, ba tare alamar za a cimma maslaha ba, ta yadda kasashe masu tasowa ke watsi da daftarin da ake amfani da shi yanzu wurin tattaunawar.
'Yan nakin, wadanda China ke jagoranta, sun ce daftarin ya aza nawaya mai yawa kan tattalin arzikin kasashe masu tasowa wajen bukatar takaita iska mai gurtaba yanayi, idan aka kwatanta nawayar da aka dora ma kasashen da su ka cigaba, wadanda su ne ma su ka fi gurbata muhulli a duniya.