Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta soma tsugunar da firsinonin Guantanamo a kasar Ghana


Firsinonin Guantanamo Bay dake kasar Cuba da Amurka ke tsare dasu tun lokacin da aka kai mata hari a shekarar 2001
Firsinonin Guantanamo Bay dake kasar Cuba da Amurka ke tsare dasu tun lokacin da aka kai mata hari a shekarar 2001

Bayan harin al-Qaida a shekarar 2001 Amurka ta bude wani wurin tsare wadanda ta kama da hannu cikin kai harin a tsibirin Guantanamo dake kasar Cuba, cikinsu ne yanzu ta sake tsugunar da wasu biyu a kasar Ghana.

Amurka ta tura firsinonin Guantanamo Bay dake kasar Cuba su biyu zuwa Ghana domin sake tsugunar dasu kamar yadda wani mai magana da yawubn Ma'aikatar Tsaron kasar ya bayyana jiya Laraba.

Firsinonin biyu 'yan asalin kasar Yamal Mahmoud Omar bin Atef da Khalid Moammed Salih al-Dhuby an tsaresu ne na tsawon shekaru 14 ba tare da gabatar dasu gaban shari'a ba ko zarginsu da wani laifi.

Bayan binciken kwakwaf a kansu ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta yanke shawarar cewa basu da wata barazanar tsaro ga Amurka.

Mai magana da yawun Pentagon yace "Amurka tana matukar godiya ga gwamnatin Ghana saboda halin jinkai da ta nuna da kuma yadda ta goyi bayan kokarin rufe sansanin Guantanamo Bay inda ake tsare mutane."

Yayinda mutanen biyu suke zaune a Ghana gwamnatin kasar zata sa ma mutanen biyu ido matuka domin ta san abubuwan da su keyi.

Ma'aikatar harkokin wajen Ghana tace mutanen an wankesu daga duk wani zargin aikin ta'adanci amma yace za'a bari su zauna cikin kasar na dan wani lokaci ne kawai.

Yace "mun nuna aniyarmu ta karban mutanen su zauna kasarmu na tsawon shekaru biyu bayan haka suna iya barin kasar".

Pentagon tace har yanzu akwai sauran firsinoni 105 a Guantanamon. Nan da 'yan makonni za'a tura wasu da dama zuwa wasu wuraren.

Rufe sansanin Guantanamo na cikin abubuwan da Shugaba Obama ya sa a gabasa ya yi kafin ya bar kujerar mulki.

To saidai 'yan majalisar wakilan kasar ba sa son su amince da rufe sansanin na Guantanamo saboda wai yin hakan na nufin baza firsinonin Guantanamo din zuwa cikin gidajen kason Amurka.

Wannan shi ne karon farko da Amurka zata tura wasu firsinonin Guantanamo zuwa nahiyar Afirka. Yawancin firsinonin da suka rage a Guantanamo din 'yan asalin kasar Yamal ne wadanda ba za'a iya mayar dasu kasar ba saboda yakin da ke gudana da kuma rashin zaman lfiya.

XS
SM
MD
LG