Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Soke "Visar" Shugabar Kotun ICC Fati Bensouda


Babbar mai shigar da kara a kotun ICC da ke Hague, Fatou Bensouda
Babbar mai shigar da kara a kotun ICC da ke Hague, Fatou Bensouda

Ofishin mai shari’a Bensouda, wacce ‘yar asalin kasar Gambia ce, ya ce zai gudanar da aikinsa ba tare da wata fargaba ba ko nuna banbanci.

Amurka ta soke takardar visar babbar mai shigar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, Fatou Bensouda, kan abin da ake ganin na da nasaba da binciken da take yi game da wasu laifuka da ake zargin dakarun Amurka da aikatawa a Afghanistan.

A jiya Juma’a, ofishin Bensouda, ya bayyana hakan, sannan wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya tabbatar da cewa lallai an soke takardun visar mai shari’a Bensouda.

Kakakin ya kara da cewa, Amurka za ta dauki duk matakan da suka dace wajen ganin ta kare ‘yancin gashin kanta, sannan da duk wani bincike na rashin adalci da kotun ta ICC za ta yi akanta.

Sai dai ofishin mai shari’a Bensouda, wacce ‘yar asalin kasar Gambia ce, ya ce zai gudanar da aikinsa ba tare da wata fargaba ba ko nuna banbanci.

Amurka da Rasha da China, ba mambobi ba ne a kotun hukunta manyanlaifuka ta ICC.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG