Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kara Kasashe 8 cikn Jerin Sunaye Masu Safarar Mutane


John Kerry, Sakataren harkokin wajen Amurka
John Kerry, Sakataren harkokin wajen Amurka

Kasar Amurka ta kara kasashe 8 a jerin sunayen kasashen da ta shigar cikin kundin batanci, domin ko, kasashen basu kokarin ganin sun dakatar da fataucin mutane zuwa kasashen Turai.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tasa kasar Uzbekistan da Turmenistan cikin jerin kasasje 27 da suka fi kowa aikata wannan danyen aikin.

Sai kuma kasashe irin su Myamer,Haiti,Djibouti,Papua, Guinea, da Sudan.

Yayin da kasashe irin su Kuwait da Thailand sune na ukun karshe a jerin sunayen kasashen, kuma an tabbatar suna kokarin ganin rage wannan fataucin mutanen, sai kuma ana sawa wadannan kasashen ido.

Sai dai maaikatar ta harkokin kasashen waje tace zaiyi wuya a iya tantance irin rawar da kasashe irin su Libya,Somalia,da Yemen keyi sabo da rin yanayin da kasashen suke ciki.

A cikin rahoton na 16 daSakataren harkokin wajen Amurka Jonh Kerry yasa ma hannu, yace fataucin mutane ya zame babban alkakai a sassan duniya daban-daban, musammam ma wadanda ake tilasta wa mata aikin karuwanci da kuma wadanda ake kawo wa da karfin tuwo domin yin anfani dasu.

Yasce muna yaki da bauta irin ta zamani wadda kusan mutane miliyan 20 ne ke huskantar wanna hukuba a sassan duniya daban-daban.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG