Jami’an tsaron Amurka da aka ambata a kaofinnyada labarai dake nan Amurka sun ce jiragen da basu da matuka za a girke su ne kusa da Niamey babban birnin kasar ta Nijar, tare da sojojin sama na AMurka kamar su dari.
A cikin wasika sanar da majalisar dokokin Amurka da ya aike wa wakilai jiya jumma’a, shugaba Obama yace za a yi amfani da jiragen ne wajen tara bayanan sirri. Shugaba Obama bai fito fili cikin wasikar ya bayyana kasar da za a girke jiragen ba, amma jami’an sojin Amurka da suka yi magana bisa sharadin ba za a bayyana sunayensu ba, sun ce galibin dakarun Amurka da suka isa Nijar ranar laraba, mayakan sama ne da zasu yi aiki domin tallafawa jiragen da basu da matuka.
Amurka da turai sun bayyana damuwar cewa mayakan sakai na kungiyar al-Qaida suna kokarin fadada ikonsu ta wajen wasu sassan yammacin Afirka barazana ga tsaron kasashen duniya.