Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi Bangarorin Da Ke Yaki a Sudan Ta Kudu


FILE - Government soldiers stand guard by their vehicle on the front lines in the town of Kuek, northern Upper Nile state, South Sudan.
FILE - Government soldiers stand guard by their vehicle on the front lines in the town of Kuek, northern Upper Nile state, South Sudan.

Kamar yadda tun farko aka nuna fargabar zai faru, fada ya sake barkewa a Sudan Ta Kudu duk da yarjajjeniyar zaman lafiyar da aka cimma.

Amurka da kawayenta na Turai sun ce mummunan sabon fadan nan da ya barke a Sudan Ta Kudu ya saba ma yarjajjeniyar zaman lafiyar da aka cimma a kasar, kuma su na kiran da a gaggauta kawo karshen fadan.

A wata takardar bayani ta hadin gwiwa da Amurka da Burtaniya da Norway, da ake kira Troika, su ka fitar jiya Laraba, sun ce fadan da ake yi a wajejen garin Yei wani mummunan karan tsaye ne ga yarjejjeniyar kwance damara da aka cimma a watan Disamba na 2017 da kuma yarjajjeniyar da aka farfado da ita wadda gwamnatin Sudan Ta Kudu da kuma kungiyoyin ‘yan tawaye da dama su ka cimma a watan Satumban da ya gabata.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ba da rahoto a makon jiya cewa fada tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun ‘yan tawaye y a raba mutane wajen 13,000 da muhallansu ta yadda wajen 5,000 su ka tsere zuwa Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (Congo).

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG