Gwamnatin Malaysia ta ce Amurka ta fara dawo mata da biliyoyin kudade da aka sace daga asusun da ake kira 1MDB.
Atoni Janar na Malaysia, Tommy Thomas, ya ba da sanarwar hakan a yau Talata, inda ya ce sun karbi kimanin dalar Amurka milliyan $57 daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ma’aikatar shari’a ta Amurka da kamfanin Red Granite Pictures, kamfanin hada fina-finai na Riza Aziz.
Karar da aka shigar akan kamfnin Red Granite Pictures, wanda ya shirya wani fim mai suna “The Wolf of Wall Street” a shekarar 2013 da jarumi Leonardo DiCaprio ya fito a ciki, an yi amfani da kudaden da aka sata daga Asusun wajen shirya fim din.
Thomas ya ce sun cimma yarjejeniyar biyan dala milliyan $60 wanda Amurka za ta rike dala miliyan $3 daga ciki don biyan ayyukkan binciken da aka gudanar.
Facebook Forum