Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta daure dan Najeriya bisa taimakawa Al-Qaida


Tutar 'Yan Al-Qaida
Tutar 'Yan Al-Qaida

Jiya Laraba wata kotun tarayya a Amurka ta yanke hukuncin daurin shekaru 22 ga wani dan Najeriya, bisa laifin farfaganda da samowa reshen kungiyar Al-Qaida da ke Yemen mayaka.

Lawal Babafemi, dan shekaru 35 da haihuwa ya amsa cewa, ya aikata laifi bara, ta wajen taimaka wa wata kungiyar ta'addancin kasar waje, wato Al-Qaida da ke shiyyar kasashen Larabawa.

Yayin da ya ke tare da kungiya mai tsattsauran ra'ayin Islama, ya yi aiki a sashin labarai, ciki har da mujallarta mai suna Inspire, a cewar masu gabatar da kara.

Ya kuma rubuta wakar 'yan gayu ta "Rap" ga kungiyar da zummar sa matasan yammacin duniya su yi sha'awar kungiyar.

Masu gabatar da kara sun ce kungiyar ta biya Babafemi kusan Dalar Amurka 9,000 don ya nemo wasu 'yan Najeriyar majiya Turanci don su shiga kungiyar ta ta'addanci.

XS
SM
MD
LG