Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta cimma yarjejeniya da Julian Assange don amsa aikata laifi guda daya na hada baki, da yada bayanan sirri ba bisa ka'ida ba, a wata yarjejeniya da ake sa ran za ta kawo karshen tuhume-tuhumen da ake yi wa Wikileaks a Amurka.
A cewar wata wasika da masu shigar da kara na Amurka suka buga, Assange zai amsa aikata laifin a wata kotun tarayya ta Amurka da ke tsibirin Mariana ta Arewa kuma ana sa ran zai koma Australia bayan zaman kotun, wanda ke nuni da cewa, masu gabatar da kara ba za su nemi alkali a yanke masa hukunci ba bayan shekaru biyar da ya shafe a gidan yarin Belmarsh na Landan yana kalubalantar tasa keyarshi Amurka.
Yarjejeniyar za ta kawo karshen tuhume-tuhumen da masu gabatar da kara na gwamnatin tarayya suka yi wa Assange a karkashin dokar leken asiri kan wallafa bayanan diflomasiyya da na soja da WikiLeaks ya yi.
Assange yana tsare a gidan yarin Belmarsh na Landan , daya daga cikin gidajen yari mafi tsaro a Burtaniya cikin shekaru biyar da suka gabata, yayin da yake kalubalantar tasa keyar shi domin fuskantar hukumci a Amurka.
Kafin wannan lokacin, Assange ya shafe shekaru bakwai a tsare a cikin ofishin jakadancin Ecuador da ke Landan, inda ya gudu a cikin 2011 don gujewa tuhumar cin zarafi da aka yi karar shi a kai a Sweden.
Gwamnatin Ecuador ta ba Assange mafaka, wanda ya ba shi damar zama a ginin ofishin jakadancin yayin da 'yan sandan Birtaniyya suka kafa turke a waje suna sanya ido su ga lekowarshi.
Gwamnatin Ecuador ta kori Assange a cikin 2019, da ya ba 'yan sandan Burtaniya damar kama shi. Wata kotun Burtaniya ta sami Assange da laifin saba sharuddan belinsa ta yanke masa hukuncin daurin makonni 50 a gidan yari. Ya kuma ci gaba da zama a gidan yarin da ke karkashin matsanancin tsaro ko da yanke ya kammala shekarun da aka dibar mashi.
Dandalin Mu Tattauna