Shugaban sojojin dake kula da harkokin sararin samaniya ya fadawa ‘yan Majalisu cewa tabbas wata rana zasu samar da sojojin sama jannati.
Idan aka amince, sojojin sama jannatin za su zamanto runduna ta shida, kuma an kirkiri rundunar farko tun alif 1947.
Sai dai kuma, Sanata Joni Ernst, daga jihar Iowa ta ce tana bukatar a tabbatar mata da cewa akwai bukatar samar da rundunar sojojin sama ta shida.
Shima dan Majalisa, Angus King daga jihar Maine, ya ce yanzu haka bashi da tabbacin cewa zai iya amicewa ko kin amincewa da sojojin sama, saboda abin da ya ce tsaron da ake dashi na sama yana aiki.
Babban hafsan hafsoshin soji Janar Joseph Dunford, ya ce “Abin da zai taimaka mana shine yadda fasahar abokan hamaiyarmu ta sama sun lalace” ya kara da cewa kasashen China da Rasha sun kirkiri fasahar da zata kare na’urorin Amurka a sararin samaniya.
Facebook Forum