Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da China Sun Kulla Yarjejeniyar Cinikayya


Shugaban Amurka Donald Trump da Mataimakin Firimiya China suna shan hannu
Shugaban Amurka Donald Trump da Mataimakin Firimiya China suna shan hannu

Jiya Laraba shugaban Amurka tare da mataimakin firimiya na China Liu He, ya sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta kawo karshen yakin cinikayya da ya kwashe watanni 18 ana yi tsakanin manyan kasashen biyu masu girman tattalin arziki a duniya.

“Wannan yarjejeniyar ce da ba wanda ya taba ganin irinta,” a cewar Trump, wanda ya yi hasashen cewa zata samar da zaman lafiya a fadin duniya.

A bikin rattaba hannun da aka gudanar jiya Laraba a Fadar White House, mataimakin firimiya na China ya karanta wata wasika daga shugaban kasar China Xi Jinping, wadda ta ce “a matakin gaba kuma, bangarorin biyu suna da bukatar aiwatar da yarjejeniyar cikin gaskiya.”

Cikin jawabinsa Liu, ya yi nuni da cewa “an sami koma baya lokacin da ake gudanar da zaman tattaunawar, amma wakilan kasashen biyu basu karaya ba.”

Amurka da China sun amince da fuskar farko ta yarjejeniyar tun watan Disamba. Wadda ta nemi China ta ‘kara sayen kayayyakin Amurka, ta kuma dakatar da abin da take yi na takurawa kamfanonin waje su mika mata fasaharsu, haka kuma kada ta ci gaba da sarrafa kudadenta domin samun garabasa wajen fitar da kayayyaki.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG