Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da China Sun Koma Bakin Dagar Cinakayya


China US Trade
China US Trade

Kamar yadda wasu kwararru su ka yi ta hasashe a baya, tattaunawar Amurka da China ta kasa kaiwa ga cimma jituwa a bangaren cinakayya. Hasali ma kasashen biyu sun koma bakin daga, kuma sun fara bugawa a fagen kasuwanci.

Amurka da China sun shiga fafatawa a fagen cinakayya, bayan tattaunawarsu ta baya-bayanan kan batutuwan cinakayya wadda har su ka kammala ba tare da cimma jituwa ba.

Ranar Jumma’a Amurka ta kara haraji daga 10% zuwa 25% kan kayakin China na kudi dala biliyan 200 da ake shigar da su Amurka. China ta ce za ta mai da martani, amma ba ta yi cikakken bayani ba.

Shugaban Amurka Donald ya kuma umurci jami’an gwamnatinsa su fara shirin kara haraji kan kusan dukkannin sauran kayakin China da ake shigar da su Amurka, wadanda kudinsu ya kai dala biliyan 300, matakin da ake ganin zai dau watanni kafin a fara aiwatarwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG