Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.
TAMBAYA
Yau za a ji kashi na biyu kuma na karshe na amsar tambayar nan mai cewa, "Assalamu alaikum VOA Hausa. Muna so ku tambaya mana masanan harkokin kasa-da kasa, kan yanda kasar Mali da Burkina Faso ke shirin kulla yarjejeniya da kasar Rasha, maimakon kasar Faranasa. Yaya lamarin zai kasance? Za a dinga koyar da harshen Rashanci a makarantun Bokon kasashen, ko za a cigaba da amfani da harshen Faransanci ne. Kasashen biyu za su dinga amfani da takardar kudin CFA, wadda kasar Faransa ke buga musu ne Ko kuwa?"
Masu Tambaya: Idan an tuna, masu tambayar su ne Babandi Mamman Bande, da Tasiu Unguwar Tudu, Damagaram da Issuhu Madatai, da Ali Sarkin yakin Ni'ma, da shugaba Iliya Maishayi Garkin Daura.
AMSA: To idan masu tambayar, da ma sauran masu sha’awar jin amsar, na tare da mu, ga kashi na biyu kuma na karshe na amsar da wakilin Muryar Amurka a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, ya samo daga wurin Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano, kamar yadda za a ji.
Sai a kasance da mu makon gobe don jin amsoshin wasu tambayoyin.
A yi saurare lafiya: