Washing, D.C. —
Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na AmsoshinTambayoyinku.
Yau za a ji kashi na biyu na amsoshin tambayoyin masu sauraronmu da dama, da su ka hada da Adamu Aliyu Ngulde, da Buhari Yahaya Nguru, da Adamu Habu Umar Taura, jihar jigawa masu son jin tarihin Abzinawa (ko Auzunawa) na Janhuriyar Nijar, musamman ma ko shin su na da alaka da wata kabila ko kuma wata kasar kuma.
To, idan masu tambayar da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, ga amsar da wakilinmu a Yamai, Sule Barma, ya samo daga masanin tarihi, Farfesa Djibo Hammani, na Jami’ar Abdou Moumouni Dioffo da ke Yamai.
A sha bayani lafiya:
Dandalin Mu Tattauna