Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu dasake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.
Tambaya:
Assalamu alaikum VOA Hausa. Don Allah mu na so ku yi mana bayani, kan wadanda Allah bai ba su haihuwa ba, kuma suka dauki marayu. Shin marayun za su iya cin gadonsu?
Masu Tambaya: Ayuba Isah da Malami Kurra daga garin Sarkin Noma, jihar Yoben Najeriya
Amsa:
To idan masu tambayar na saurare, ga babi na daya na amsar da mu ka samo ma ku daga Shugaban Majalisar Malaman Izala Shiyyar Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, kuma Sarkin Malaman Duguri, Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, wanda ya ma fadada amsar, tare da yin shinfida. A latsa a yi saurare lafiya: