Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYIKU: *Me ya sa wasu sassan duniya ke fama da ambaliya a daidai lokacin da wasu ke fama da fari? *Tarihin Hausawan Sudan ii


Ibrahim K Garba
Ibrahim K Garba

Yau ma mun samo ma ku amsoshin tambayoyi masu kayatarwa kan yadda ake fama da ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya alhalin kuwa ana matukar fari a wasu sassan. Akwai kuma kashi na biyu na amsar tambaya kan Hausawan Sudan.

Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu dasake saduwa a wannan shirin na amsoshintambayoyinku.

TAMBAYA 1:

“Assalamu Alaikum VOA Hausa. Don Allah ku tambaya Mana masana muhalli, dalilan da su ka jawo samun fari a wasu kasashen da ke yankin Kuryar Afurka, da ma wasu yankuna na kasar China dake nahiyar Asia; lokacin da wasu kasashen duniya suke fama da ambaliyar ruwa.”

Mai Tambaya: Aminu Adamu Mallam Madori, Jihar Jigawa, Najeriya.

TAMBAYA 2

(Za kuma a ji kashi na biyu na amsar tambayar nan mai cewa): “Salam Muryar Amurka. Don Allah Ina son ku ba ni tarihin Hausawan kasar Sudan. Shin akwai wani banbanci tsakanin Hausawan kasar Sudan da na Najeriya?

Mai Tambayar: Idan an tuna, shi ne Babangida IBB Giyawa daga Karamar Hukumar Mulki ta Gwaranyo jahar Sokoto, Najeriya.

MASU BAYAR DA AMSOSHIN

Amsa 1. To bari mu fara da amsar tambaya kan yadda akan fuskanci fari a wurare irin Kuryar Afurka da sassan Asiya, a daidai lokacin da kuma wasu sassan duniya ke fama da yawan ruwa har ma da ambaliya. Idan mai tambayar, Malam Aminu Adamu Malam Madori, da ma sauran masu sha’awar jin amsar na tare da mu, wakilin Muryar Amurka a Agadez, Hamid Mahmud ya samo amsa daga wani masanin yanayi da ke Agadez, Malam Abubakar Nufi’u, kamar yadda za a ji a sautin.

Amsa 2: Sai kuma kashi na biyu na amsar tambaya kan banbancin Hausawan Sudan da na Najeriya. Idan mai tambayar, Babangida IBB Giyawa da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, ga kashi na biyun na amsar da wakilinmu a shiyyar Adamawa, Muhammad Salisu lado, ya samo daga Malam Ibrahim Musa Audu na Kwalejin Horas Da Malamai ta jihar Adamawa da ke Hong, wanda zai dan koma baya kan inda ya yi bayani a makon jiya.

Sai a danna sautin a saurari cikakken shirin:

10-08-22 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU -.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:04 0:00
XS
SM
MD
LG