Laminu Idris, dan asalin jihar Zamfara, wanda yake gudanar da karatunsa a matakin digirin-digirgir a fannin lissafi a jami'ar Sheffield dake Ingila ya shaidawa DandalinVOA cewa yana gudanar da bincike akan yadda za'a iya gano dalilan da sukes a cututtuka dake addabar mutane ke bijirewa magunguna.
Fannin lissafi yana taimakawa wajen gano adadin sinadarai da ake amfani dasu wajen hada magunguna, da kuma gano hanyoyi da za'a yi amfani da kassafin wajen ganin nau'ukan sinadiran da ake amfani dasu a kowace cuta yayi dai-dai da cutar.
Don ta hanyar lissafi ne kawai za'a iya gano matsala da kuma yadda za'a magance ta, wanda yake kara nuni da cewar shi lissafi ya shafi rayuwar duniya baki daya, domin kuwa babu wani abu da za'a iya yi a rayuwar yau da kullun ba tare da anyi amfani da lissafi ba wajen saita al'amurran yau da kullun.
Duniya na cigaba ne ta amfani da manhajar lissafi a bangarori dabam dabam. Sai a tara don jin yadda tattaunawar ta kasance da bakon namu a wanna makon.
Facebook Forum