Shugaba Salva Kiir ya ayyana dokar ta-baci a wasu sassan Sudan ta Kudu inda ambaliyar ruwa ta raba sama da mutane miliyan daya da muhallansu.
Yawancin wadanda ambaliyar ruwan ta rutsa da su, mazauna yankunan Bahr el Ghazal da Upper Nile ne.
Yayin wani taron manema labarai da aka yi a Juba a ranar Larabar da ta gabata, Ministan Harkokin kula da ayyukan agaji da daukan matakan ko-ta-kwana, Hussein Maar Nyuot, ya ce ambaliyar ta lalata daruruwan gonaki.
A wani labari makamancin wannan, Gwamnatin Somaliya da kungiyoyin ba da agaji na Majalisar Dinkin Duniya, sun yi kira da a kai agaji don taimakawa dubban ‘yan kasar ta Somaliya da ambaliyar ruwa ta fi shafa a cikin shekarun da suka gabata.
Wani kwamitin ba da agajin gaggawa na gwamnati ya ce ruwan sama mai karfin gaske shi ya haifar da ambaliyar ruwan, wanda ya sa ruwan kogin Juba da yankin Shabelle, suka cika suka tumbatsa a yankunan da ake kira Bay da Bakool.