Allah Ya yiwa sarki Abdullah na kasar Saudi Arabiya rasuwa. Sarkin ya dade yana kulla kawance da Amurka a yakar ta’addanci.
Ana kyautata zaton shekarunsa 90 a lokacin da ya rasu, kuma ya share lokuta masu tsawo yana jinya.
Kaninsa Yarima Salman wanda ba daga daki daya suka fito ba, shine zai gaje shi. Salman wanda ake kyautata zaton shekarunsa 79 dama shine yarima mai jiran gado, sannan shine ministan tsaron kasa tun shekara ta 2012.
Shugaba Barack Obama a madadin Amurkawa ya aika da sakon ta’aziyya zuwa ga jama’ar Saudi da iyalan marigayin. Mr. Obama yace Sarkin ya kamanta gaskiya, kuma yana rike alkawuran da ya dauka, musamman anfani da kawancen Amurka da Saudiyya wajen wanzar da zaman lafiya da walwala.
Sarki Abdallah wanda a hukumance ya haye karagar mulki a shekara ta 2006, ya rike shugabanci ne tun shekara ta 1995, biyo bayan cutar cutar ajali da ta kama dan uwansa Sarki Faud a lokacin.