WASHINGTON DC, —
Tsohon Sifeta Janar Alhaji Muhammad Yusuf Dikko, wanda aka fi sani da MD Yusuf, Allah yayi mishi rasuwa jiya da yamma a birnin tarayya Abuja. Ana sa ran za'ayi jana'izar shi a garin shi na haihuwa yau da safe.
Shi dai MD Yusuf ya yi aikin dan sanda wanda har ya kai matsayin sifeta janaral a Najeriya kimanin shekaru 35 da suka wuce, wanda daga bisani ya shiga siyasa wanda har yayi takara shugabancin Najeriya, amma Allah bai bashi nasara ba.
Marigayi MD Yusuf, sanannen mutu ne me gaskia da son jama'a, da fatar Allah yayi masa rahama yasa aljanna tzama makomarshi amin.