A shirin Domin Iyali na wannan makon, wakilinmu Lamido Abubakar ya yi hira da wakilan kungiyar kare hakkokin mata da kananan yara WRAPA a jihar Zamfara, Zainab Nuhu jami’ar gudanarwa, da kuma Dahiru Mohammed jami’in ayyuka na kungiyar, dangane da batun zargin da wadansu iyaye suka yi a Kaurar Namoda cewa, wani dan shekaru talatin da ya bata karamar ‘yarsu ‘yar shekaru biyu.
A cikin hirarshi da Shirin Domin Iyali, Kakakin Rudunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara SP Shehu Mohammad ya tabbatar da cewa, 'yan sanda sun kai karamar yarinyar asibiti bayan samun rahoton yi mata fyade, kuma gwajin da aka gudanar ya tabbatar da cewa, babu shakka an yi mata fyade. Ya kuma ce sun kama wanda ake zargin mai suna Kabiru Nasiru.
Ga bayanin da jami'an kungiyar WRAPA na jihar Zamfara su ka yi wa shirin Domin Iyali
Facebook Forum