WASHINGTON, DC —
Batun kare hakkin kananan yara na daya daga cikin batutuwan da Majalisar Dinkin Duniya take dauka da muhimmanci da ya sa aka rattaba hannu kan kuddurori da kuma kulla yarjejeniyoyin daukar makatan inganta rayuwar kananan yara. Sai dai shekaru bayan amincewa da wadannan kudurorin, har yanzu galibin yara a kasashe masu tasowa suna rayuwa cikin mawuyacin hali.
A yau shirin Domin Iyali zai haska fitila kan irin wannan lamarin, inda a jihar Plateau aka kona wadansu kananan yara bisa zargin maitanci. Ga abinda daya daga cikin yaran da zamu saya sunan
sa, ya shaidawa Shirin Domin Iyali.
Facebook Forum